IQNA

Majalisar Dokokin Iraki Ta Kasa Zaben Shugaban Kasa

22:35 - March 31, 2022
Lambar Labari: 3487109
Tehran (IQNA) A jiya Laraba ne majalisar dokokin Iraqi ta gudanar gudanar da zamanta domin zaben shugaban kasar, wanda shi ne na biyu cikin kasa da mako guda, amma duk da hakan lamarin ya ci tura.

Wata sanarwa da sashen yada labarai na majalisar ya fitar ya bayyana cewa, shugaban majalisar wakilai Muhammad al-Halbousi ne ya bude zaman taro na shida.

Wakilai da dama daga jam’iyyun siyasa daban-daban sun kaurace wa zaman majalisar da aka sadaukar domin zaben shugaban kasar, musamman kawancen "Coordination Framework".

Wakilai 200 ne kawai suka halarci zaman majalisar, yayin da zaben shugaban kasar Iraki ke bukatar kuri'ar kashi biyu bisa uku na 'yan majalisar, wato akalla wakilai 220 daga cikin 329.

Wannan shi ne karo na biyu da ake gudanar da zaman, bayan da majalisar dokokin ta kasa zaben shugaban kasa a ranar Asabar din da ta gabata, saboda rashin samun cikakkun kuri’u, bayan da wakilai kusan 126 suka kaurace wa zaman.

'Yan takara 59 ne ke fafatawa a zaben shugaban kasar Iraki, musamman dan takarar jam'iyyar Patriotic Union of Kurdistan (PUK) Barham Salih da dan takarar jam'iyyar Democratic Party (KDP), Reber Ahmed.

Saleh yana samun goyon bayan ‘yan siyasa da dama, musamman "Coordination Framework", yayin da Ahmed ke samun goyon bayan kawancen "Save a Homeland" mai kujeru 175.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4045748

 

captcha