Tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, kungiyar jihadul Islami ta mayar da martani dangane da kisan da Israi'ila ta yi wa wani matashi bafalastine a yankin Jabal Sabih da ke cikin gundumar Nablus a Falastinu.
Kakakin kungiyar Jihadul Islami Tarik Salma ya bayyana cewa, irin matakan da Isra'ila take dauka domin murkushe matasan Falastinawa da suke hana ta yin kutse a cikin yankunansu, hakan ba zai yi tasiri ba, domin hakan shi ne ke kara karfafa gwiwar matasan wajen yin gwagwarmaya da zaluncin Isra'ila.
A jiya ne sojojin Isra'ila suka harbe Ahmad Bani Shamsa matashi dan shekaru 16 da haihuwa a kusa da garin nablus, a lokacin ad matasan suka hana sojojin yahudawa kutsa kai a cikin yankuannsu.
A nasa bangaren shugaban kungiyar Jihadul Islami Ziyad Nakhala ya bayyana cewa, matasan Falastinawa za su ci gaba da yin tsayin daka a gaban duk wani aikin wuce gona da iri da ta'addanci irin na Isra'ila, domin kuwa kisa ba ya tsorata matasan Falastinawa wajen kare hakkokinsu da al'ummarsu.