IQNA

Malaman Addini A Mauritania Sun Bada Fatawar Haramta Kulla Hulda Da Gwamnatin Isra'ila

23:26 - February 01, 2021
Lambar Labari: 3485611
Tehran (IQNA) manyan malaman addini a Mauritania su 200 ne suka fitar da fatawar haramta hulda da Isra’ila a matsayin mahangar addinin musulunci.

Jaridar Ra'ayul Yaum ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da majalisar dokokin kasar Mauritania take kira ga gwamnatin kasar, ta kafa dokar haramta hulda da Isra’ila, manyan malaman addini a kasar kimanin 200 ne suka fitar da fatawar haramta hulda da Isra’ila .

Malaman sun amince da wannan fatawar ce a wani taron da suka gudanar a masallacin taufik da ke birnin Nuwakshot babban birnin kasar. Malaman sun kara da cewa hulda da Isra'ila  goyon baya ne ga ta’asar da take aikatawa a kan Falastinu da kuma kisa da rushe rushen gidajensu da take yi.

Kafin haka dai wasu kafafen yada labarai na Isra'ila da kuma Amurka sun bada rahoton cewa kasashen Mauritania da Indonesia suna cikin jerin kasashen Larabawa da musulmin, wadanda za su samar da hulda da gwamnatin yahudawan Isra'ila a nan gaba. 

3951412

 

captcha