Shafin yada labarai na My Joy Online ya habarta cewa, a cikin wani bayani da ya fitar, Sheikh Usman Nuhu Sharubutu babban limamin kasar Ghana ya bukaci musulmi da suka gudanar da bukukuwan salla babba a cikin gidajensu domin kaucewa kamuwa da cutar corona.
Malamin ya bayyana hakan en a cikin bayanin da mai magana da yawunsa ya fitar, ida ya bayyana cewa ya zama wajibi jama’a su kiyaye dukkanin ka’idojin da aka gindaya domin kare kai daga kamuwa da cutar corona ko kuma yada ta.
Ya cea kan wannan dalilin en ma aka dakatar da gudanar da abubuwa da dama, da suka hada har sallar jam’i da kuma wasu taruka da kuma halartar makarantu.
A ranar 31 ga wata Yuli ne dai za agudanar da babbar salla a kasar Ghana.