IQNA

Shugaban Masu Addinin Gargajiya A Ghana Ya Soki Lamirin Masu Sukar Akidarsa

17:55 - July 19, 2020
Lambar Labari: 3484999
Tehran (IQNA) Shugaban masu bin addinin gargajiya a yankin Somanya da ke cikin Yilo Krobo a gabashin Ghana ya caccaki masu sukar al’adunsu.

A cikin bayanin da ya gabatar,  Shugaban masu bin addinin gargajiya na New Gavriel Enlightenment Traditional a yankin Somanya ya bayyana cewa, dukkanin mutanen kasar Ghana suna da hakkin su yi addinin da suke bukata.

Ya ce a  bisa imaninsu, kowane dan adam yana da matsayi wurin ubangiji, kuma dole ne sauran ‘yan adam su girmama mutum da mahangarsa, idan aka yi haka kowa zai zauna lafiya kuma ya yi abin da ya fahimta, ba tare da samun  wata matsala a tsakanin ‘yan adam ba.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, kundin tsarin mulkin Ghana na shekara ta 1992 ne ya bayar da dama ta yin kowane irin addini ko bin kowace irin akida a matsayin mutum na dan kasa.

Wasu daga cikin al’ummomin Ghana suna bayyana irin wadannan al’adu an masu bin addinin gargajiya da cewa ba abu ne mai kyau ba, kuma suna kira da a haramta wannan addini.

Sai dai bisa la’akari da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya ba su dama, ba a bu ne mai sauki a iya hana yin hakan ba, duk kuwa da cewa wasu daga cikin musulmi da kiristoci suna adawa da abin da ake yi a cikin wannan addini na gargajiya a kasar.

3911103

 

captcha