IQNA

Saka Kiran Sallla A Masallatan Aljeriya Domin Yaki Da Corona

23:52 - April 07, 2020
Lambar Labari: 3484687
Tehran (IQNA) ma’aikatar harkokin addini ta kasar Aljeriya ta sanar da cewa akwai shirin fara saka karatun kur’ani a dukkanin masallatan kasar.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a yau ma’aikatar harkokin addini ta kasar Aljeriya ta sanar da cewa akwai shirin fara saka karatun kur’ani a dukkanin masallatan kasar kasar domin tunkarar annobar corona. 

Bayanin yace manufar hakan ita ce samar da yanayi na natsuwa a tsakanin al’ummar musulmi na kasar, sakamakon mawuyacin halin da ake ciki na yaduwar mummunar annoba.

Ma’aikatar ta ce ta gabatar da wanann bukata ga gwamnati domin amncewa da ita, kuma da zaran an amince da hakan daga yau Talata za a fara aiwatar da shirin.

Za a rika saka karatun kur’ani na wasu lokuta a dukaknin masallatai, mintuna talatin bayan kiran salla, kasantuwar an dakatar da sallolin Juma’a tun makonnin da suka gabata.

 

https://iqna.ir/fa/news/3889748

 

 

captcha