IQNA

An Saka Masallacin Hilmi A Cikin Wuraren Tarihi Na Masar

23:52 - January 01, 2018
Lambar Labari: 3482258
Bangaren kasa da kasa, an saka masallacin Abbas Hilmi da ke birnin Alkahira na kasar Masar a cikin wuraren tarihi na wannan kasa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na egyptday cewa, wannan masallaci an gina shi ne tun a shekara ta 1893, wanda sarki Abbas Hilmi Pasha ne ya gina shi.

Bisa dokar kasar Masar duk wurin yah aura shkaru daro da ginawa to ya shiga cikin wuraren tarihin kasar.

Kasar Masar dai tana daga cikin kasashen duniya da suka shara wajen yawan kayan tarihi da kuma wurare masu tsohon tarihi na duniya.

A wurin ginin wannan masallaci dai an yi amfani da fasaha ta musamman a lokacin, wanda kuma har yanzu ana kallon wurin a matsayin wurin da ke nuna irin dadaddiyar fasar da al’ummar kasar suke da ita tun tsawon zamunna.

3678289

 

 

captcha