IQNA

An Tarjama Littafin Imam Gharib A Cikin Harshen Turkancin Istanbuli

23:54 - August 02, 2017
Lambar Labari: 3481760
Bangaren kasa da kasa, an tarjama littafi mai suna Imam Gharib da aka rubuta kan Imam Ridha (AS) a cikin ahrshen turkancin Istanbuli.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, bangaren yada labarai na cibiyar yada al’adun muslucni ya sanar da cewa, an tarjama wannan littafin ne bisa kokarin cibiyar Alhuda wadda kan gudanar da ayyuka a matsayi na kasa da kasa.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan littafi yana bayani kan yadda Imam Ridha (AS) ya kasance a lokacin da ya karbi mukamin yarima mai jiran gado na khalifan zamaninsa na abbasiyawa, da kuma hikimar da take tatatre da yin hakan.

Kasantuwar Imam Ridha (AS) ya karbi wannan matsayi hakan bai sauya komai ba daga irin zaluncin da limaman gidan manzon Allah suka fuskanta daga sarakunan zamaninsu, amma Imam yayi hakan ne bisa dalilai na hikima, wanda hakan kuma ya kare mabiya tafarkin iyalan gidan manzo zuwa wani dan lokaci har zuwa shahadarsa.

Imam Ridha (AS) ya yi amfani da wannan damar wajen isar da sakon Allah madaukin sarki daga cikin fadar azzalumai, duk kuwa da irin matakan kange shi daga jama’a.

3626301


captcha