IQNA

Salah Zawawi A Zantawa Da IQNA:

Martanin Kasashen Musulmi Dangane Da Abin Yake Faruwa A Aqsa Ya Kasa

20:59 - July 30, 2017
Lambar Labari: 3481750
Bnagaren kasa da kasa, jakadan Palastinu a birnin Tehran Salah Zawawi ya bayyan cewa ko shakka babu martanin da kasashen musulmi suka mayar dangane da keta alfarmar aqsa bai wadatar ba.
Salah Zawawi a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayyana cewa, hakika sun yi zaton cewa gwamnatocin kasashen musulmi a wannan karon za su motsa wajen takawa Isra'ila birki kan cin zarafin msuulmin palastinu da kuma keta alfarmar masallacin Aqsa mai alfarma, amma dai har yanzu ba ta canja zane ba.

Ya ci gaba da cewa tun kafin wannan lokaci bisa tsawons hekarun da aka kwashe ana cin zarafin palastinawa, akwai kasashe da suka dage wajen nuna goyon bayansu ga al'ummar palastinu da kuma wurare asu tsarki, kuma har yanzu wasu daga cikinsu suna nan akan bakansu.

Jakadan na palastinua Iran ya ce yana jinjinawa jamhuriyar muslunci ta Iran dangane da irin namijin kokarin da take wajen kare hakkokin palastinawa duk inda ta samu kanta, wanda hakan shi ne ke tabbatar da cewa matsain Irn a akan batun palastinu ba mai sauyawa ba ne.

Haka nan kuma ya kirayi sauran musulmi masu 'yanci da su zama tsintsiya daya madaurinki dayawa wajen kare manufofin da suka shafi al'ummar musulmi da ake zalunta a palastine, domin kuwa a cewarsa, rashin hadin kan musulmi da kuma rarrabuwarsu a kan lamurra da dama shi ne ya jawo musu rauni, kuma hakan ya karfafa makiyansu.

3623920


captcha