Al'ummar Palasdinu tana nuna rashin amincewarta da matsin lambar da ake yi musu a duk lokacin da su ke son shiga masallacin.
Wannan mataki dai yana zuwa ne sakamakon yadda wasu daga cikin gwamnatocin larabawa suke ci gaba da nuna halin ko in kula da ta'addancin Isara'ila a kan wurare masu tsarki da suka hada da masallacin aqsa alkiblar musulmi ta farko.
Haramtacciyar kasar Isra'ila na ci gaba da cin karenta babu babbaka a kan wannan wuri mai tsarki ne tare da hana musulmi yin salla ta hanyar kafa musu ka'idoji masu tsauri da cin zarafinsu, wanda hakan yasa ala tilas musuli suke ci gaba da kauarace ma yin salla a cikin masalalci, duk kuwa da cewa a jiya yahudawan sun sanar da bude shi, tare da bayar da damar shiga ciki bisa sharadin da suka gindaya.
Masallacin Aqsa Na Ci Gaba Da Kasancewa Karkashin Mamaya