IQNA

Gangami Mai Taken Daga Haifa Zuwa Aqsa A Palastinu

23:17 - May 07, 2017
Lambar Labari: 3481492
Bangaren kasa da kasa, Palastinawa sun fara gudanar da gangami mai taken daga Haifa zuwa Aqsa da nufin kara tabbatar da rashin amincewarsu da mamaye musu kasa da yahudawa suka yi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran SAFA cewa, an fara gudanar da gangamin a yau a dukkanin yankunan Palastinawa da suke karkashin mamayar yahudawan Isra’ila tun daga shekara ta 1948.

Daya daga cikin malamai masu gwagwarmaya a Palastinu Sheikh Ra'id Salah na daga cikin wadanda suke jagorantar wannan gangami a gabashin masallacin Aqsa, kamar yadda a sauran yankunan gabar yamma da kogin Jordan ma Palastinawa suna gudanar da wannan gangami.

Babbar manufar hakan ita ce tabbatar wa yahudawan Isra’ila da cewa Palastinawa ba za su taba amincewa da mamayar da aka yi ma kasarsu tare da kafa Isra’ila ba.

Masu gangamin sun yi ta rera taken neman ‘yanci da Allawadai da mamayar Isra’ila a kan kasarsu, da kuma yin kira ga sauran al’ummomin duniya da su mara baya ga al’ummar palastinu da ake zalunta tsawon tarihin wannan karni.

3597045


captcha