IQNA

Zaman Taro Kan yaki Da Ta’addanci A Kasar Sudan

23:39 - August 18, 2016
Lambar Labari: 3480722
Bangaren kasa da kasa, an bude wani zaman taro a yau a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan da zimmar ganin an kara samun wayewar kai dangane da batn ta’addanci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, shi dai wannan zaman taro da aka bude a yau a birnin Khartum bisa zimmar ganin an kara samun wayewar kai dangane da batun ta’addanci da kuma yadda za a yi yaki da shi, ya hada bangarori na kasa da kasa.

Haifa Abu Ghazala shi ne babban sakatare na bangaren hulda da jama’a da yada labarai a cikin kungiyar kasashen larabawa ya bayyana cewa, kungiyar ce ta dauki nauyin shirya wannan taro.

Ya ci gaba da cewa, yanzu akwai manyan baki da suke halrtar taron da suka hada har da ministocin yada labarai na wasu daga cikin kasashen larabawa.

Babban abin da ake tatatunawa dai shi ne samar da hanyoyi na bai daya da za su taimaka wajen ganin an yaki ta’addanci musammana cikin kasashen larabawa, da kuma dakile kungiyoyi da suke dauke da akidar ta’addanci.

Fauzi Alghawil shi ne babban darakta na kwamitin hulda da jama’a da yada labarai na kungiyar kasashen larabawa ya bayayna cewa, suna burion ganin abubuwan da za a tattauna awannan taro su yi tasiria cikin kasashen larabawa wajen dakile yan ta’adda da suka addabi al’umma awannan lokaci.

Da dama daga cikin masana dai sun yi amannar cewa, babbar hanyar yaki da ta’addanci ba amfani da makami ba ne, domin ko an kashae ‘yan ta’adda matukar dai akidar ta’addanci tana nan a cikin littafai da kuma a cikin kalaman wasu malamai da kuma fatawoyinsu na halasta ayyukan ta’addanci, babu yadda za a iya shawo kan wannan matsala, domin ko an gama da wasu za su tashi.

A kan haka masu wanann ra’ayin ke ganin cewa ya kamata ne a yi fada da akidar daga tushenta na wahabiyanci, wanda kuma an kasar da take yada wannan akida a duniya, wanda daga nan kuma ake samar da yan ta’adda.

3523601

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna khartum sudan taro lokaci wahabiyanci
captcha