IQNA

An Kame Wani Dan Takfir Mai Wulakanta Kur’ani A Tunisia

23:58 - February 02, 2018
Lambar Labari: 3482359
Bangaren kasa da kasa, an kame wani dan ta’addan takfiriyya da ke wulakanta kur’ani a kasar Tunisia.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na arralmia.com cewa, ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar Tunisia ta sanar da cewa, jami’an tsaro sun samu nasarar kame wani dan ta’addan takfiriyya da ke wulakanta kur’ani a kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa, jami’an tsaron sun kai samame ne a gidan nasa, inda suka samu wasu tarin kwafin kur’ani mai tsarki da ya yi rubuce-rubuce a cikinsu, tare da tozarta wannan littafi mai tsarki.

Jami’an tsaron sun samu bayani kan irin halin da ake ciki ne dagane da wannan mutum da kuma abin da ya aikatawa, da kuma alakarsa da kungiyoyin ‘yan ta’adda na wahabiyawa, wanda ya tabatar da cewa yana sato wadannan kwafin kur’anai ne daga masallatai daban-daban.

Yanzu haka dai jami’an tsaro sun mika wannan mutum ga kotu, inda ake tuhumarsa da tozarta kur’ani da kuma yin sata a cikin masallatai.

3687638

 

 

 

 

 

captcha