IQNA

Hannun Jarin Saudiyya Ne Silar Yaduwar Wahabiyanci A Tunisia

18:06 - October 02, 2016
Lambar Labari: 3480817
Bangaren kasa da kasa, sakamakon saka kudade masu tarin yawa da Saudiyya ke yi a kasar Tunisia hakan ya sanya wahabiyanci yana yaduwa a kasar matuka.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hukumar yada aladun musulunci cewa, masarautar yalan gidan Saud na yin amfani da kudade domin yada akidar wahabiyanci a cikin kasar Tunisia.

Shugaban ofishin yada al’adun muslunci Asadi Movahad ya bayyana cewa, Iran tana kokari wajen ganin an yada sahihiyar koyarwa irin ta addinin muslunci da manzon Allah (SAW) tare da yaki da tsatsaran ra’ayi wanda ke kai wasu zuwa ga ta’addanci, wand kuma hakan shi ne haikanin abin da akidar wahabiyanci take koyarwa.

Ya kara da cewa sun fitar da fim wanda yake Magana a kan tarihin musulunci da kuma abin da ya faru na kisan kiyashin da aka yi wa mahajja a shekarar da ta gabata, wanda hakan bai yi wa mahukuntan wahabiyawa dadi ba ko kadan.

Dangane da abubuwan da suke faruwa na hanoron hada al’ummar musulmi fada kuwa, ya bayyan acewa ko shakka babu wannnan aiki ne na yahudawa da suka bayar da kwangilarsa ga wahabiyawa, wadanda su ne wakilansu a cikin musulmi.

Daga karshe ya bayyana cewa ya zama wajibi kan al’ummar musulmi bai daya su zama cikin fadaka da kuma sanin hakikanin abin da yake faruwa, domin kaucewa fadawa cikin tarkon da aka dana musu domin rusa su daga cikin gida.

Maukuntan wahabiyawa dai suna yin iyakacin kokarins domin yada akidar wahabiyanc a cikin kasashen musulmi, da nufin tabbatar da cewa duniya ta fahimci musulunci ne a kan koayrwar wannan akida, wadda ta ginu a kan kafirta musulmi da kiransa mushriki da sauransu, wanda hakan ne ya haifar da kungiyoyin ya ta’adda da suka addabi dniya a halin yanzu.

3533103


captcha