IQNA

Mai Fatawa Na Al-Saud

Maulidin Manzo (SAW) Shirka Ne Girmama Ranar Kasar Kuma Wajibi Ne

11:05 - September 28, 2016
Lambar Labari: 3480815
Bangaren kasa da kasa, malaman wahabiyawan Saudyya sun ce maulidin manzon Allah (SAW) shirka ne, taron ranar kasa kuma wajibi ne.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar alalam cewa, babban mai bayar da fatawa na masarautar wahabiyawa ta al saud Abdulaziz alsheikh ya bayyana taron maulidin manzon Allah (SAW) da cewa aiki ne na shirka.

Mutumin ya yi kira ga matasa wahabiyawa musamman da su yi hattara da shiga cikin duk wani abu mai alaka da maulidi domin kuwa a cewarsa ba shi da wani tushe a cikin musulunci bidi’a ce da aka kirkira wanda kuma yin hakan kafirci ne da shirka.

Amma dangane da tarukan zagayowar ranar da turawa suka kafa masarautar alsaud, Alsheikh ya bayyana wannan rana da cewa ran ace ta kasa baki daya, kuma dole ne a raya ta da taruka na tunawa da kafa wannan masarauta.

Ya ci gaba da cewa wannan ran ace da ya zama wajibi a kan dukkanin yan kasa da su taru su yi godiya ga Allah kan wannan babban alkhairi da ya yi musu na samun kafa masarautar iyalan gidan Saud.

3533546

captcha