IQNA

‘Yan Ta’addan Daesh Sun Sanar Da Talata A Matsayin Ranar Idi

15:57 - September 11, 2016
Lambar Labari: 3480775
Bangaren kasa da kasa, ‘yan ta’addan takfiriyya masu dauke da aidar wahabiyanci na Daesh sun ce Talata ce Idi ba Litinin ba.
Kamfanin dilalncin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na shafaqna cewa, kungiyar 'yan ta'adda masu dauke da akidar kafirta al'ummar musulmi Takfiriyyah Wahabiyyah na ISIS, sun fitar da bayani da ke cewa; Ranar gobe Litinin ce ranar Arafa, Talata kuma ranar sallar Layya, tare da tabbatar da cewa duk wanda ya yi aikin ranar Arafa a yau Lahadi ko kuma ya yi salla gobe Litinin, to ya kafurta.

Bayanin ya ce dole ne dukkanin yankunan da suke a karkashin abin da suke kira daular muslunci da su yi aiki da abin da aka sanar, idan kuma ba hakan za a hukunta duk wanda ya sabawa hakan.

Kamar yadda kuma bayanin na Daesh ya kara da cewa, yin aiki arafa a Lahadi ko kuma yin salla a gobe Litinin aiki na ridda, duk muusulmi da ya yi hakan ya fita daga addinin mulsunci akan haka ne suke son ganin sun banbanta kansu da murtaddai.

Wannan bayani dai ya shafi dukkanin yankunan da suke karkashin ikon wannan kungiya ne da cikin Iraki musamamn a Mausil da kewaye, inda suke gudanar da mulki irin na tatsinanci.

Bangaren bayanin y ace daga cikin hukunci da za ayi wa wadanda suka gudanar da ayyukan arafa a yau ko kuma suka yi salla a gobe litinin, awai bulala da kuma yin gin gidan kaso a matsayin hukunci na abin da suka kira shari’a.

Fatawar ta ‘yan ta’addan dai ta yi hannun riga da fatawar babban malamin akidar wahabiyawa da ke bayar da fatawa ga gidan sarautar wahabiyawa na al Saud, wanda ya tabbatar da yau Lahadia matsayin ranar arafa gobr ranar sallar idin layya.

3529639


captcha