IQNA

Shehunnan Wahabiyawa Sun Shelanta Yaki kan iran Da Rasha

20:40 - October 07, 2015
Lambar Labari: 3383019
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin shehunnan wahabiya sun kira da su hada kai domin yaki da kasar Rasha da kuma Iran sakamakon kashin da ‘yan ta’adda ke sha a Syria.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta (RT) cewa, wasu daga cikin malaman wahabiya da ke dauke da mummnar akidar nan ta kafirta musulmi, sun sa hannu domin yaki da kasar Rasha da kuma Iran sakamakon kashin da ‘yan ta’adda ke sha a Syria a hannun dakarun kasar ta Rasha a cikin kwanakin nan.

Sun bayyana yaki a kan gwamnatin Syria da cewa yaki ne mai tsarki, kuma suna kira da a yaki Rasha saboda tana kashe masu dauke da akidar kafirta musulmi da ke al’ummar Syria da sunan jihadi.

Wahabiyawan da suka sa hannun sun kai 55, yayin da ita kuma Rasha ta gargadi wasu larabawan yankin tekun fasha dangane da shirinsu na aikewa da makamai masu kakkabo jiragen yaki zuwa ‘yan ta’adda a Syria.

Shafin kamfanin dillancin labaran ya nakalto daga shafin yada labarai na Ra’ayul Yaum cewa, ma’aikatar tsaron kasar Rasha da aike da wasu sakonni a asirce zuwa ga ofisoshin jakadancin wasu kasashen larabawan yankin teken fasha da ke shirin aikewa da wasu makamai zuwa ga ‘yan ta’addan Syria, da ke shirin bayar da makamai masu kakkabo jirage ga ‘yan ta’addan.

Rahoton ya ce sakon na Rasha ya kunshi gargadi ga wadannan kasashe kan su san cewa abin da suke shirin yi yana da matukar hadari, kuma hakan ba zai hana Rasha ci gaba da abin da ta sanya gaba na ragazgaza sansanonin ‘yan ta’adda a Syria ba, domin hakan ne kawai zai kawo karshen ta’addancin da ke neman rusa kasar tare da mayar da miliyoyin mutane ‘yan gudun hijira, wadanda a da suke zaune lafiya a kasarsu.

Gwamnatin Rasha ta yi watsi da kiran da kasashjen turai da na wasu larabawa gami da Turkiya suke yi mata, na ta dakatar da kai hari kan sansanonin ‘yan ta’adda, domin yin hakan zai karfafa Bashar Assad da ba su dasawa da shi, yayin da Rasha ta sha alwashin cewa ba za ta bar kasashen turai da na larabawa su sake yin abin da suka yi a wasu kasashen a kan Syria ba.



3382777

Abubuwan Da Ya Shafa: wahabiyawa
captcha