IQNA

Azhar ta Yi Allawadai Da hana Musulmin China Yin Azumin Ramadan

23:47 - June 20, 2015
Lambar Labari: 3316533
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar Azhar ta yi kakkausar suka da yin Allawadai kan matakin da mahukuntan kasar China suka dauka na hana musulmi a wani yankin kasar yin azumin wanann shekara.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, Ahmad tayyib sheikhul Azhar ya yi kakkausar suka da yin Allawadai kan matakin da mahukuntan kasar China suka dauka na hana musulmi a wani yankin kasar yin azumin wanann shekara ba tare da yin la;akari da cewa wannan bangare ne na addininsu ba.

Ya ci gaba da cewa dole ne mahukuntan China sun sake shawara dangane da daukar irin wadannan matakai marassa kan gado kan musulmi, wannan dais hi ne karon farko da gwamnatin kasar ta China ta fito fili ta shekanta cewa ta hana musulmin kasar yin azumi saboda wasu dalilai.

Wanann mataki dai yana ci gaba da fuskantar maratani daga al’ummomin musulmi daga koina cikin fadin duniya, lamarin da ake ganin zai tasiri matuka wajen tilasta China yin nazari kan irin wananna mataki na Karen tsaye da take yi kan addinin muslunci da musulmi.

3316417

Abubuwan Da Ya Shafa: china
captcha