IQNA

A shirye-shirye Gasar cin kofin duniya na Qatar An yi wa bangaye ado da hadisan annabci

15:36 - November 01, 2022
Lambar Labari: 3488104
A daidai lokacin da ake shirin fara gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da ake yi a kasar Qatar, kasar ta kafa zane-zane da dama a cikin birnin da kuma muhimman wurare da aka kawata da hadisan manzon Allah a cikin harsunan Ingilishi da na Larabci domin gabatar da addinin Musulunci ga masu kallon wasannin. wadanda suka zo daga ko'ina cikin duniya..

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, kwamitin shirya gasar cin kofin duniya na shekarar 2022 a kasar Qatar ya sanar da cewa, a daidai lokacin da gasar cin kofin duniya ke gabatowa, an kafa zane-zane a kan titunan birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar tare da hadisai na annabta da tarjamarsu zuwa harshen turanci.

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun wallafa hotuna da yawa da ke nuni da cewa a ko'ina a kan tituna da muhimman wurare a birnin Doha, akwai zane-zane da aka kawata da hadisan annabci masu daraja, wadanda ke bayyana ruhi da jigon addinin Musulunci da kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW).

Kafofin yada labaran kasar Qatar sun bayyana cewa, wannan shiri na neman gabatar da addinin muslunci ne ga wadanda suka zo Qatar daga sassan duniya domin kallon gasar cin kofin duniya da za a fara ranar 20 ga watan Nuwamba.

Qatar ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya ta 2022 daga ranar 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga Disamba kuma ita ce kasar Larabawa ta farko da ta karbi bakuncin wannan gasar kwallon kafa ta kasa da kasa.

 

4096072

 

captcha