Mustafa Waziri, babban sakataren majalisar koli ta adana kayayyakin tarihi na kasar Masar, ya ce sashen tarihi na filin jirgin sama na birnin Alkahira ya gano wasu rubuce-rubuce 13 da aka rubuta su tun daga karni na 17, 18 da 19, tare da nade su tare da wasu kudade na zamanin Daular Usmaniyya.
Dangane da yadda za a gano da kuma kwace wadannan kayayyakin tarihi, ya ce: “Sashen kayayyakin tarihi na filin jirgin sama na Alkahira sun samu sanarwa daga hukumar ‘yan sandan tsaron fasinja cewa ana zargin daya daga cikin kayayyakin da fasinjojin yana dauke da kayan tarihi ne.
Sannan kuma kwamiti na musamman na kula da kayayyakin tarihi na koli a Majalisar Dokokin kasar, ya dora wa daya daga cikin ammbobinsa bin kadun wanan lamari, domin gano hakikanin asalin wadannan kayan tarihi.