Kamfanin dillancin labaran Iqna, kungiyoyin farar hula ne na kasar Amurka suka kirayi jerin gwanon a birnin New York, wanda ya samu halartar dubban jama’a.
A yayin jerin gwanon an daga kwalaye da aka yi rubutu a kansu, da ke kira ga gwamnatin India da ta kawo karshen nuna wariya ga musulmi a kasar.
Haka nan kuma masu jerin gwanon sun yi gangami a gaban karamin ofishin jakadancin India da ke birnin New York, domin isar da sakonsu kai tsaye ga mahukuntan kasar ta India.
Zanga-zangar ta samu halartar musulmi da wadanda ba musulmi, da kungiyoyi masu zaman kansu da lauyoyi masu fafutuka da sauransu.
https://iqna.ir/fa/news/3874693