IQNA

Kuwait Ta Yi Allawadai Da Rusa Gidajen Falastinawa Da Isra’ila Ke Yi

23:57 - July 25, 2019
Lambar Labari: 3483880
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Kuwait ta yi Allawadai da kakausar murya kan rusa gidajen Falastinawa da Isra’ila ke yi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran KUNA cewa, wani babban jami’i a ma’aikatar harkokin wajen kasar Kuwait ya bayyana cewa, gwamnatin kasar tana yin Allawadai da kakausar murya kan rusa gidajen Falastinawa da Isra’ila keyi a cikin kwanakin nan.

Ya ce wannan abu da Isra’ila take yi ya hannun riga da dukkanin dokoki da kaidoji na kasa da kasa baki daya.

Wanann jami’i na Kuwait ya ce yanzu haka kasarsa tana tattaunawa tare da Afrika ta udu da kuma Indonesia a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya kan wannan batu.

Kasashen uku suna da shirin gabatar da daftarin kudiri ga kwamitin tsaro domin gudanar da zama, kan irin abin da Isra’ila take na rusa gidajen falastinawa ba gaira ba sabar, domin daukar matakin mata mata burki.

 

3829840

 

 

 

captcha