IQNA

Hizbullah: Rusa Gidajen Falastinawa Na A Matsayin Laifukan Yaki

23:47 - July 24, 2019
Lambar Labari: 3483875
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar Hizbullah ta bayyana rusa gidajen Falastinawa da Isar’ila ke yi a matsayin laifukan yaki.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Shafin yada labarai na tashar Almanar ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da kungiyar Hizbullah ta fitar a jiya, baya ga yin Allawadai da kakkausar murya dangane da rusa gidajen Falastinawa da Isra’ila ke yi, ta bayyana hakana  matsayin laifin yaki.

Bayanin ya ce abin da yake faruwa a halin yanzu na rusa gidajen Falastinawa a gabashin birnin Quds domin gina matsugunnan yahudawa ‘yan share wuri zauna, ya sabawa dukkanin dokoki na duniya daga ciki kuwa hard a dokokn majlaisar dinkin duniya.

Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, idan kasashen duniya suka ci gaba da yin gum da bakunansu a kan wannan ta’asa da Isra’ila take tafkawa, to hakan yana a matsayin lasisi ne a gare ta da ke halasta mata aikata barna.

A cikin makonnan ne Isra’ila ta fara aikin rusa gidajen Falastinawa a gabashin birnin Quds, domin gina matsugunnan yahudawa a cikin yankunan, wanda shi ne shiri mafi girma na rusa gidajen Falastinawa tun daga shekara ta 1967.

3829299

 

captcha