IQNA

Jagora: Hajji Aiki Ne Na Ibada Kuma Yake Damfare Da Siyasar Musulmi

22:54 - July 03, 2019
Lambar Labari: 3483803
Jagoran juyin juya halin musluci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana aikin hajji a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan ibada da Allah ya farlanta kan musulmi, a lokaci guda kuma aiki ne da yake damfare da siyasar al’ummar musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na ofsishin jagora ya sanar da cewa, a lokacin da yake ganawa da jami’ai masu kula da ayyukan hajji na kasar Iran a yau, jagoran juyin juya halin musluci Ayatollah sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa; aikin hajji yana a matsayin babban gishiki daga manyan jinshikai na addinin muslunci, wanda kuma yake bayyana siyasar al’ummar musulmi da karfinsu da daukakarsu.

Ya ce ko shakka babu aikin hajji aiki ne na ibada wanda yake tattare da hikimomi na ubangiji, duk kuwa da cewa mafi yawan abubuwan da ke cikinsa kwaikwayon aiki wasu daga cikin manyan bayin Allah ne, amma kuma Allah ya farlanta shi a kan al’ummar musulmi.

Jagoran ya ce babban abin da ke cikin aikin hajji shi ne tarbiyantar da ruhi da kuma kaskantar da shi a gaban Allah madaukakin sarki, wanda kuma hakan hanya ce ta tsakake ruhi, wadda Allah yake wanke bayinsa daga zunubai, tar da sanya su cikin inuwar rahmarsa.

Ya ci gaba da cewa, akwai masu cewa mene ya hada aikin hajji da siyasa? Ya ce aikin hajji a cikin addinin muslucni yana tattare da siyasa, domin kuwa shi ne wurin da musulmi suke bayyana matsayinsu a kan dukkanin lamarin siyasar duniya.

A wurin aikin hajji ne musulmi suke jaddada imaninsu da kuma yin riko da tafarkin ubangiji shi kadai, tare da barrata daga mushrikai wadanda suka cutar da su kuma suka hana su bautar Allah kafin hijira zuwa Madina, kuma wannan sunna ta Allah da manzo tana nan a cikin ibadar hajji har abada.

Ya ce har yanzu musulmi suna fuskantar zalunci da danniya da cin zarafi, amma rashin hadin kansu da rarrabarsu ta sanya ba za su iya nisanta kansu daga makiya addini da ke hankoron rusa musulmi ba, duk kuwa da cewa a hajji dole ne a bayyana karba kiran ubangiji, kuma a baranta daga makiya ubangiji, kamar yadda yake a cikin addini tun lokacin ma’aiki.

3824086

 

 

captcha