IQNA

Hamas Na Kokarin Kafa Wata Hadaka Domin Bijirewa Yarjejeniyar Karni

22:57 - April 26, 2019
Lambar Labari: 3483581
Kungiyar Hamas ta sanar da cewa, tana shirin hada kan bangarori daban-daban domin samar da wata babbar Hadaka, wadda za ta kalubalanci abin da ake kira yarjejeniyar karni.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, shafin yada labarai an Palastine Yaum ya bayar da rahoton cewa, a jiya Talata an gudanar da wani zaman taro da Hamas ta kira a garin Gaza, tare da halartar wakilan kungyoyin Falastinawa, da suka hada da Jihadul Islami, jabhat sha’abiyya da sauransu, inda aka tattauna kan hadarin da ke tattare da abin da ake kira yarjejeniyar karni.

Salah Bardawil wani babban kusa ne a kungiyar Hamas, ya fadia  wajen taron cewa; ba za su taba amincewa da makircin da ake kitsa wa al’ummar Palastine da sunan yarjejeniyar karni ba, kuma suna nan suna daukar matakai na fuskantar wannan makirci.

Bardawil ya kara da cewa, Hamas tana tuntubar kungiyoyin falastinawa da kuma wasu gwamnatocin wasu kasashe, gami da kungiyoyi na kasa da kasa, domin samar da babbar Hadaka wadda za ta kalubalanci wanann shiri da ake kira yarjejeniyar, wanda yake nufin kawo karshen batun mayarwa Falastinawa da hakkokinsu, tare da tabbatar da halascin mamayar Isra’ila  a kan Palastine.

3805941

 

 

captcha