IQNA

Afirka Ta Kudu Ta Ce Ba Ta Canja Siyasarta Ba Dangane Da Isra’ila

23:55 - September 27, 2018
Lambar Labari: 3483015
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin Afrika ta kudu ta ce har yanzu tana kan siyasarta dangane da Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wani bayani da ta fitar a jiya, ma’iaktar harkokin wajen kasar Afrika ta kudu ta jaddada cewa, har yanzu ba ta canja matsayinta dangane da Isra’ila ba.

Bayanin ya ce Afirka ta kudu na kallon ain da Isra’ila take yi a kan Falastinawa a matsayin zalunci da mamaya da kuma nuna musu fin karfi, inda take ganin cewa dole ne a warware wannan matsala ta hanyar adalci, ba tare da tauye wa Falastinawa hakkokinsu ba.

Tun a ikin watan mayun da ya gabata ne dai Afirka ta kudu ta kirayi jakadanta da ke Isra’ila, domin nuna rashin amincewa da mayar da ofishin jakadancin Amurka a birnin Quds.

3750754

 

 

 

captcha