IQNA

Tarukan Tunawa Da Zagayowar Rasuwar Imam Khomeini (RA)

23:55 - June 04, 2018
Lambar Labari: 3482725
Bangaren siyasa, dubbban daruruwan jama’a ne suka taru yau a hubbaren marigayi Imam Khomeini (RA) domin tunawa da zagayowar lokacin wafatinsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau dubun-dubatar jama’a ne suka taru yau a hubbaren marigayi Imam Khomeini (RA) domin tunawa da cika shekaru ashirin da tara da wafatinsa.

A wannan karon dai lokacin ya zo daidai lokacin da ae gudanar da taruka na shahadar Imam Ali (AS) wanda hakan ya sanya tarukan suka zama biyu a lokaci guda, duk kuwa da cewa taron shahadar Imam Ali (AS) dama ya kasance ne bisa lissain hijira kamariyya kuma  acikin watan Ramadan.

Imam Khomeini (RA) ya kasance shi ne jigon juyin juya halin musulunci a Iran, duk da cewa ya kasance daya daga cikin manyan malaman mazhabar ahlul bait (AS) amma kuma  a lokaci guda ya jagoranci al’ummar Iran wajen kawar da gwamnatin ‘yan amshin shata ga turawa, tare da kafa ‘yatacciyar gwamnati bisa turba ta addini.

Dukkanin al’ummar Iran sun baiwa Imam goyon baya wajen kifar da gwamnatin ‘yan kanzagin Amurka, amma kuma Imam Khomeni bai dorawa mutane zabinsa ba, ya bayar da dama ga dukkanin al’ummar Iran da su kada kuri’ar raba gardama domin zabar irin sarin da suke so gwamnati ta kasance a kansa.

Fiye da kashi casa’in da takwas na al’ummar Iran sun zabi tsarin musulunci, wanda kuma a kansa ne aka kafa manufar juyin juya halin musulunci.

3720332

 

captcha