IQNA

Batun Bahrain Na Daga Cikin Ajandar Taron Kare Hakkin Bil Adama Na UN

22:31 - February 26, 2018
Lambar Labari: 3482431
Bangaren kasa da kasa, batun cin zarain bil adama a kasa Bahrain na daga cikin muhimman ajandodin taron hukumar kare hakkin bil adama ta majalisar dinkin duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalro daga shafin jaridar lu’ulu’a cewa, daga cikin muhimman ajandodin taron hukumar kare hakkin bil adama ta majalisar dinkin duniya har da batun cin zarain bil adama a kasa Bahrain.

Antonio Guterres da kuma wasu daga manyan jami’an majalisar dinkin dniya za su haarci taron wanda za a bude a yau a babban ifishin hukumar da ke brnin Geneva na kasar Switzerland.

A zaman taron za a tattauna muhimman batutuwa ne da suka shafin cin zarain ‘yan adam, da gallaza wa fursunonin siyasa, kisan kiyashi da laifukan yaki da sauran batutuwa masu kama da hakan a kasashen duniya, wanda kuma batun Bahrain yana kan gaba a cikin abubuwan da taron zai mayar da muhimmanci a kansu.

Masarauta kama karya ta Bahrain dai ta jima tana gallaza wa ‘yan adawar siyasa masu kira zuwa ga adalci da kawo karshen mulkin kama karya a kasar, inda masarautar ke ta hankoron mayar da batun na bangarancin mazhaba.

3694642

 

 

 

captcha