IQNA

An Mayar Da Ayatollah Isa Kasim Zuwa Gidansa Bayan Tiyata

23:08 - February 04, 2018
Lambar Labari: 3482364
Bangaren kasa da kasa, bayan gudanar da wani aikin tiyata da aka yi masa, Ayatollah Isa Kasim ya koma gidansa da ake killace da shi.

An Mayar Da Ayatollah Isa Kasim Zuwa Gidansa Bayan TiyataKamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Lu'ulua cewa, a jiya Ayatollah Isa Kasim ya koma gidansa da ake killace da shi bayan gudanar da wani aikin tiyata da aka yi masa.

Bayanin ya ci gaba da cewa jami'an tsaron masarautar kama karya ta kasar Bahrain suka dauki Ayatollah Isa Kasim daga asibitin da ak ayi masa tiyata shekaran jiya, inda suka mayar ad shi gidansa da ake killace shi.

Tun daga ranar 23 ga watan Mayun shekara ta 2017 ne mahukuntan masarautar kama karya ta Bahrain suka sanya karnukan farautarsu suka kaddamar da farmaki kan gidan babban malamin addini na kasar Ayatollah Isa Kasim, tare da kashe biyar daga cikin almajiransa da kuma kame wasu, kuma tun daga lokacin suke ci gaba da killace gidan.

Babban laifin shehin malamin a wurin masarautar kama karya ta Bahrain dai shi ne, yana yin nasiha ga sarakunan kasar kan su ji tsoron Allah su adalci a tsakanin mutanenta da suke jagoranta.

3688297

 

 

captcha