IQNA

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Suka Kan Kisan Musulmi A Afirka Ta Tsakiya

19:27 - May 21, 2017
Lambar Labari: 3481536
Bangaren kasa da kasa, majalisar dinkin duniya ta yi kakkausar suka dangane da kisan musulmi da wasu 'yan bindiga mabiya addinin kirista ke yi a Afirka ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin zerohedge cewa, jaridar Guardian ta bayar da rahoton cewa, akalla mutane ashirin da biyu suka rasa rayukansu a cikin sabon rikici da ya barke a arewa maso gabashin Jumhoriyar Afirka ta tsakiya.

Mataimakin Kwamandan Dakarun wanzar da zaman lafiya na majlaisar dinkin duniya a kasar Afirka ta Tsakiya diane corner a jiya Assabar na cewa fada tsakanin mayakan Saleka da na Anti Balaka a garin Bria na Jihar haute-Kotto dake arewa maso gabashin kasar yayi sanadiyar mutane ashirin da biyu tare da jikatta wasu sha bakawai na daban.

A yayin da yake bayyani kan wajibcin dakatar da wannan rikici, Mistan Diane Corner mataimakin Kwamandan Dakarun wanzar da zaman lafiya na majlaisar dinkin duniya ya tabbatar da cewa fadace-fadacen da ya wakana cikin wannan maku da muke ciki yayi sanadiyar yin hijra na fararen hula kimanin dubu goma a garin Bria.

Tun a Shekarar dubu biyu d sha uku ne kasar Afirka ta tsakiyan ta fada cikin rikicin kabilanci da na addini, bayan juyin milkin da ya gudana a kasar, lamarin da ya janyo tsananin rashin tsaro tare da lakume rayukan mutane da dama.

3601207


captcha