IQNA

Musulmin Italiya Sun Yin Allawadai Da Harin Birnin Faris Na Faransa

23:33 - January 11, 2015
Lambar Labari: 2697506
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslnci a kasar Italiya da dama ne suka fito suka yi Allahwadai da harin da aka kai kan kamfanin jaridar kasar Faransa a cikin wannan mako.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar PressTV cewa, a cikin wanann mako mabiya addinin muslnci a kasar Italiya da dama ne suka fito suka yi Allahwadai da harin da aka kai kan kamfanin jaridar kasar Faransa tare da nisanta ayyukan ta’addanci da addinin muslunci.
Jami'an tsaron Faransa sun bayyana cewar sun kashe mutumin da ya yi garkuwa da wasu mutane a wani kantin sai da kayayyaki a gabashin birnin Paris, bayan da suka sanar da kashe 'yan uwa guda biyun nan da ake zargi da kai hari ga mujallar Charlie Hebdo ta kasar a ranar Laraba da ta gabata bayan kawanyan da suka yi musu a wajen da suka buya; kamar yadda kuma wata majiyar.
Rahotannin sun ce tun a safiyar yau ne dai jami’an tsaron na Faransa suka yi kawanya wa wadannan mutanen wadanda aka ce suna da alaka da kungiyar Al-Qa’ida bayan harin da mutane biyu suka kai ofishin wannan mujallar inda suka kashe mutane sha biyu.
Jami'an Amurka da na Tarayyar Turai dai sun bayyana cewar mutanen suna da alaka da kungiyar Al-Qa’ida saboda suna da tabbacin cewa daya daga ya taba zuwa kasar Yemen a shekarar dubu biyu da sha daya  domin neman horon a wajen ‘yan kungiyar a’idan.
Jami’an kasashe daban-daban na duniya dai suna ci gaba da Allah wadai da wadannan hare-hare, to sai dai da dama suna ganin wadannan hare-hare da aka fara kai wa kasashen Turan a matsayin wata alama ta kaikayi ne ya fara komawa kan mashekiya saboda hannun da kasashen yammacin suke da shi wajen kirkiro wadannan kungiyoyi.
2696457

Abubuwan Da Ya Shafa: paris
captcha