IQNA

Taron Malaman Musulmin Kasashen Yankin Latin Amurka A Birnin Istanbul

21:32 - November 17, 2014
Lambar Labari: 1474381
Bangaren kasa da kasa, an gudanr da wani zaman taro na malaman musulmi daga kasashen yankin latin Amurka a birnin Istanbul na kasar Turkiya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na World Bulletin cewa, a jiya aka kammala gudanr da wani zaman taro na malaman musulmi daga kasashen yankin latin Amurka a birnin Istanbul na kasar Turkiya domin tattauna muhimman batuuwa da suka shafe su da kuma sanin matsalolinsu da yadda za a magance su.

Taron ya samu halartar malamai kimanin 70 daga kasashen latin Amurka, wadanda suka tattauna halin da suke ciki musamman a kasashen da suka fi yawa duk kua da cewa su ne marassa rinjayea  cikin wadannan kasashe, da suka hada da Brazil, Venezuela, Colombia, Haiti, Hondoros, Jamaoca, Cuba da kuma Contrica.

Haka nan kuma taron ya yi dubi dangane da irin gudunmawar da ya kamata mahalartansa su bayar wajen wayar da kan matasa musulmi da suke zaune a cikin wadannan kasashe, domin samun tarbiya irin ta addinin muslunci, ganin irin banbancin dabiu da al'adu na mutanen da suke zaune tare da su, da kuma tasirin da hakan zai iya yi a cikin rayuwarsu.

Dangane da batun adin kai tsakanin dukkanin al'ummar musulmi kuma, taron ya yi tsokaci irin rawar da malamai za su iya takawa a wannan bangare, domin tabbatar da cewa an samu ci gaba ta wannan fuska, musamman ma dai a tsakanin musulmin yankin.

1473577

Abubuwan Da Ya Shafa: istanbul
captcha