IQNA

Gasar Kur'ani Ta Kasar Iraki Tare Da Halartar Mahardata Kur'ani 500

23:45 - June 05, 2021
Lambar Labari: 3485986
Tehran (IQNA) mahardata kur'ani mai tsarki 500 ne ke halartar gasar kur'ani ta kasar Iraki da aka fara gudanarwa.

Shafin yada labarai na dar-alquran.org  ya bayar da rahoton cewa, A;li Hadi Kazem daraktan cibiyar kula da harkokin kur'ani a hubbaren Imam Hussain (AS) ya bayyana cewa, a halin yanzu mahardata kur'ani mai tsarki 500 ne ke halartar gasar kur'ani ta kasar Iraki da aka fara gudanarwa karkashin kulawar cibiyar.

Ya ce tun a ranar Laraba da ta gabata ce aka fara gudanar da gasar, kuma har yanzu ana cikin mataki na farko ne, kafin zuwa mataki na gaba.

Mahalartan sun fito ne daga jihohi 12 na kasar ta Iraki, kuma an kafa kwamiti karkashin hubbaren Imam Hussain (AS) wanda shi ne yake kula tare da daukar nauyin dukkanin abin da ya shafi wannan gasa ta kur'ani.

 

3975692

 

captcha