IQNA

Ana Ci Gaba Da Mayar Da Martani Kan Shirin Mayar Da Ginin Hagia Sophia Zuwa Masallaci a Turkiya

22:40 - July 11, 2020
Lambar Labari: 3484972
Tehran (IQNA) Rajab tayyib Erdogan ya amince da matakin da kotu da ta dauka na yanke hukuncin da ya bayar da damar a mayar da gizin Hagia Sophia zuwa masallaci.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, ana samun gagarumin martani a ciki da wajen Turkiyya kan shawarar Shugaba Erdogan na mayar da daya daga cikin gine-gine mafi shahara a duniya  Hagia Sophia da aka gina shekaru 1500 a matsayin coci da ke birnin Santambul zuwa masallaci, wanda a 1453 daular Usmaniya ta fara mayar das hi masallaci.

Sai dai a 1934 Kamal Ataturk ya mayar da shi zuwa wurin tarihi maimakon masallaci, wanda kuma har zuwa yanzu a akn haka yake.

Wannan matakin ya zo ne bayan wani hukuncin kotu da ke mara baya ga Shugaba Erdogan kan mayar da tsohon cocin zuwa masallaci, duk kuwa da cewa dai 'yan adawa a kasar sun yi watsi da wannan hukunci.

Bayan hukuncin da kotun ta yanke, shugaban kasar ta Turkiya Rajab Tayyib Erdogan ya bayyana cewa, mayar da wannan wuri zuwa masallaci abu ne da ya shafi sha’anin cikin gida na kasar Turkiya, a matsayinta na kasa mai cin gishin kanta.

Sai dai wanann mataki yana ci gaba da shan martani daga bangarori daban-daban na duniya, inda kusan dukaknin kasashen turai da ma wasu kasashen da ba na turai ba suka yi tir da Allawadai da hakan.

Ita ma a nata bangaren hukumar kula da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya a ta bakin kakakinta Matthieu Guevel, ta mayar da martani kan wannan lamari, inda ya ce hukumar ba ta yi maraba da wannan shawara ta hukumomin Turkiyya ba, inda ya ce da ya kamata ne kafin yanke wannan shawara a tuntubi sauran bangarori da suke da alaka da wannan wuri domin yanke shawara tare da su.

https://iqna.ir/fa/news/3909816

 

captcha