IQNA

Rashin Zuwa Aikin Hajjin Bana Zai Jawo Wa Kamfanonin Jigilar Alhazai Asarar Dala Miliyan 400 A Najeriya

23:53 - July 06, 2020
Lambar Labari: 3484957
Tehran (IQNA) Sanarwar da mahukuntan Saudiyya suka bayar kan takaita aikin hajjin bana, zai jawo asarar kudade da za ta kai dala miliyan 400 ga kamfanonin jgilar alhazai a Najeriya.

Rahotanni daga Najeriya sun sun ce a cikin wata sanawa da bangaren kula da harkokin jigilar alhazai a Najeriya ya fitar, ya bayyana cewa kamfanonin da suke jigilar alhazai a kasar za su tafka  asara a bana wadda za ta kai ta kimanin dalar Amurka miliyan 400, sakamakon rashin halartar alhazai daga Najeriya a wannan shekara.

Bayanin ya ce an karbi kudade daga maniyyata da dama da suke nufin gdanar da aikin hajjin bana, wanda kuma abin da ya biyo baya ya sanya dole a mayar musu da kudadensu.

Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da cewa wasu kamfanonin sun yi amfani da kudaden wajen shirye-shiryensu kamar yadda suka saba yi a kowace shekara, wanda hakn ke nufin sun yi asara.

 

 

3908970

 

captcha