IQNA

Za A Maka Jaridar Saudiyya A Kotu Kan Cin Mutuncin Ayatollah Sistani

23:16 - July 05, 2020
Lambar Labari: 3484955
Tehran (IQNA) Kungiyar lauyoyin Iraki ta sanar da cewa za ta shigar da kara kan jaridar Saudiyya da ci zarafin babban malamin addini Ayatollah Sistani.

Kungiyar lauyoyin Iraki a reshenta na birnin Najaf ta sanar da cewa, tana shirya kara da za ta shigar a gaban kotu bisa tuhumar jaridar Sharq Al-ausat ta kasar Saudiyya da cin zarafin babban malamin addini na kasar Iraki.

Kafofin yada labarai na kasar Iraki sun bayar da rahotannin cewa, a jiya Ali Shaibani, babban lauya a kasar Iraki, kuma shugaban kungiyar lauyoyin kasar reshen lardin Najaf ya fitar da sanarwar da ke cewa, yanzu haka sun shirya dukkanin abubuwan da za su gabar a gaban kotu domin gurfanar da wannan jarida.

Sanarwar ta ce cin zarafin abubuwa da mutane suke girammawa na addini da hakan ya hada da malamai da suke da matsayi na addini a wurin jama’a, hakan ya sabawa kowace doka ta duniya, a kan haka kungiyar lauyoyi ta kasar Iraki ba za ta zura ido a kan wannan lamari ba.

Tun bayan da jaridar ta Sharq Al-ausat ta gwamnatin kasar Saudiyya ta yi wani zanen batunci da cin zarafi ga babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani a ranar Juma’a da ta gabata, lamarin ke ci gaba da shan kakkausar suka daga bangarori daban-daban na duniya, yayin da kuma wasu suke kallon hakan a matsayin wani sabon makircin makiya addini na haifar da wata fitina a tsakanin musulmi.

Ayatollah Sistani dai shi ne mutum mafi girman matsayi na addini a kasar Iraki, wanda dukkanin malamai da ‘yan siyasa da ma gwamnatin kasar gami da shugabannin kabilu na larabawan kasar suke saurara masa.

3908567

 

captcha