IQNA

Jerin Gwanon Kin Amincewa Da Mamamayar Isra’ila A Kan Yankunan Falastinawa A Italiya

23:14 - July 05, 2020
Lambar Labari: 3484954
Tehran (IQNA) an gudanar da jerin wano a Italiya  domin nuna adawa da shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa.

Rahotanni daga Italiya sun ce, a birane 16 kasar ne a yau aka gudanar da jerin gwano domin nuna adawa da shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan.

Rahoton ya ce daga cikin wadanad suka shiga jerin gwanon har da tsohon firayi ministan kasar ta Italiya Masimo Dalma, wanda ya sheda wa manema labarai cewa, manufar hakan ita ce nuna adawa da shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa, wanda ya sabawa dukkanin dokokin duniya.

Ya ce abin mamaki ne yadda kafofin yada labarai na kasashen turai suka yi gum da bakinsu kan wannan shiri, da kuma adawar da yake fuskanta daga al’ummomin duniya.

 

 

3908823

 

 

captcha