IQNA

An Bankado Shirin Daesh Na Kai Hari A Samirra Iraki

23:57 - July 03, 2020
Lambar Labari: 3484950
Tehran (IQNA) Dakarun Hashdusshabi na kasar Iraqi sun bada sanarwan gano wani sansanin horar da mayakan Daesh a arewacin lardin bagdaza a yau jumma’a.

Shafin yanar gizo na Shafiq News ya nakalto Ali Al-Jaburi kwamandan bataliya na 42 na dakarun Hashdushabi yana bada sanarwan hakan a safiyar yau Jumma’a.

Al-Jaburi ya kara da cewa a jiya Alhamis ne dakarunsa tare da taimakon sauran jami’an tsaron kasar ta Iraqi na sama dana kasa suka fara wani shiri na tsarkake arewacin lardin Bagdaza daga mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh.

Har’ila yau Al-Jaburi ya kara da cewa mayakan na Daesh suna amfani da sansanin na karkashin kasa da ke garin Attarimiyya daga arewacin larandan Bagadaza ne don horar da mayakansu.

Banda haka ya ce dakarun da yake shugabanta sun kama mayakan na Daesh guda biyu, wadanda dama ana nemansu. Sannan an gano makamai da kuma wasu kayakin yaki a hannunsu.

 

 

3908308

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh iraki yan taadda harin samirra bankado
captcha