IQNA

Jagora: Iran Ta Yanke Kauna Daga Kasashen Turai

21:25 - September 26, 2019
1
Lambar Labari: 3484088
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya ce; Iran ba za ta taba amincewa da Amurka da kuma wasu daga cikin kasashen turai ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, jagoran ya bayyana hakan ne yau a lokacin da yake ganawa da shugaba da kuma mambobin majalisar zabar jagora  a kasar ta Iran, inda ya jaddada cewa babu wani abu da Amurka take da shi da za ta iya yaudarar Iran, kamar yadda kuma kasashen turai ba za su zama amintattu a  wurin Iran ba.

Ya ce babbar matsalar kasashen turai ita ce gajiyawa a gaban Amurka, sun nuna tsoro da kuma shayin Amurka, saboda haka ba su da ‘yanci da hurumin yin abin da Amurka ba ta yarje musu yin sa ba, a kan haka ba su zama masu amincin da za a dogara da su ba.

Dangane da alaka tsakanin Iran da kasashen turan kuwa, jagoran ya bayyana cewa, kofa bude take domin tatatunawa tsakanin Iran da kowace kasa ta duniya, in banda Amurka da kuma Isra’ila, hatta kasashen turan babu matsala danagne da tattaunawa da su, amma ba za su amince da kasashen da suka kiyayya ga Iran daga cikinsu ba.

Dangane da kalaman da jami’an gwamnatin kasar Amurka suke yia  cikin ‘yan kwanakin nan na kara kakaba takunkumi kan kasar ta Iran kuwa, jagoran ya bayyana hakan da cewa ba sabon lamari ba ne a  gare su, kuma hakan shi ne ke kara wa kasar karfi wajen kara himma da kuma dogaro da kanta.

Ya ce babbar manufar Amurka ita ce raba Iran da duk wani abu da ya ginu kan akidar juyi da ‘yanci na siyasa da tattalin arziki da kuma ci gaban kasa da al’ummarta, wanda hakan shi ne zai mayar da Iran ta sake komawa ‘yar amshin shata kamar yadda ta kasance kafin juyi, wanda kuma tunanin hakan da jami’an Amurka suke yi tamkar mafarki ne, domin kuwa ba abu ne mai yi wuwa kasar da samu cikakken ‘yanci ta koma ‘yar amshin shata ba.

Dangane da matsalolin da kasar take fuskanta kuwa sakamakon takunkumin Amurka, jagoran ya bayyana cewa dole ne jami’an gwamnati su kara zage dantse domin tunkarar hakan ta hanyar kara bunkasa ayyukan cikin gida, ta fuskar kere-kere, da masana’antu da kuma dogaro da abin da ake samarwa a cikin gida fiye da na kasashen ketare.

3845075

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Shehu sani
0
0
Mutare daku Iran kuma zamutaimaka taduk hanyar dayadace
captcha