IQNA

An Hana Alhazan Congo Sauke Farali A Bana

22:55 - July 27, 2019
Lambar Labari: 3483886
Bangaren kasa da kasa, Hukumomin kiwan lafiya na Saudiyya, sun haramta wa musulmin jamhuriya Demokuradiyya Congo, zuwa kasar domin sauke farali a bana.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Saudiyya ta ce ba zata baiwa musulmin na DR.Congo, dake son zuwa aikin hajji bana takardar biza (Visa) ba.

Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya, ta ce ta dauki matakin ne saboda barazanar yaduwar cutar a yayin aikin hajji inda mulyoyin musulmi ke taruwa ko wacce shekara a irin wannan lokaci.

Wasu kungiyoyin malamai a kasar ta DR.Congo, sun ce sun damu da matakin, amma mataki ne da ya dace kuma yake kan ka’ida.

Aikin hajji, wanda ake shirin faraway a cikin makwanni masu zuwa, na daga cikin shika-shikan musulinci guda biyar, bayan azumin watan Ramadana, zakka, sallah, da kuma Kalmar shahada.

Cutar Ebola wacce ta bulla a watan Agustan bara a DRC, ta yi ajalin daruruwan mutane.

A kwanan baya dai hukumar lafiya ta duniya, ta ayyana cutar da barazana ga duniya.

3830117

 

captcha