IQNA

Yin Allawadai Da Kalaman Wariya Na Trump Bai Isa Ba

23:54 - July 26, 2019
Lambar Labari: 3483883
Bangaren kasa da kasa, Iham Omar ‘yar majalisar dokokin kasar Amurka ta bayyana yin tir da kalaman wariya na Trump bai wadatar ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin arabi 21 cewa, Ilham Omar ta rubuta wata makala wadda jaridar Nw Yor Times ta buga, a cikin makalar tana cewa, sau da yawa mutanen gari su ne suke yaudaruwa da kalaman nuna wariya ko kyamar wani jinsia  cikin jama’a.

Ta ce haka lamarin yake a duk lokacin da aka samu bullar masu irin wannan tunani ba kasafai ake samun masana suna yaudaruwa da hakan, kamar yadda ko a Amurka ma ‘yan kasa na gari da sukan san kimar kasarsu, basa cin zarafin ko nuna masa kyama.

Ilham Imar ta ce abin da ya fi muni shi ne yadda kasa kamar Amurka shuganta ne yake da irin wannan akida, ta nuna kyama da wariya ga wani jinsi, saboda dalilai na bangaranci ko dai na launin fata ko addini ko kuma asalin da ban a Amurka ba.

Ta e dole ne Amurkawa su mike domin kare kasasu daga gurbacewar tunani, tare da hana yaduwar irin wanann akida ta Trump a tsakanin al’ummar Amurka.

 

 

 

3830021

 

 

 

captcha