IQNA

An kai Hare-Hare A kasar Sri Lanka a Majami’oi Da Ote-Otel

23:47 - April 21, 2019
Lambar Labari: 3483563
Wasu rahotanni na cewa a yau an kai hari a kasar Sri Lanka  akan majami’oi da otel-otel tare da kashe mutane da ma.

Kamfanin dillancin labaran iqna iqna, Rahotanni daga Sri Lanka na nuna cewa mutum akalla 130 suka mutu, kana wasu da dama suka raunana a wasu jerin hare hare da aka kai a wasu otel-otel da kuma majami’u.

Alkalumman farko farko da aka fitar sun ce mutum 42 sun mutu a Columbo, babban birnin kasar, inda aka kai hari kan wasu otel otel na katsaita da kuma wani coci.

Ko baya ga hakan kuma an kai wani hari kan wani coci dake yankin Batticoloa dake gabashin kasar inda mutum akalla 10 suka rasa rayukansu.

Bayanai daga kasar sun ce an kai harin kan majami’in ne a daidai lokacin da jama’a ke ibada a yayin bikin ista.

Babu wata kungiya data dau alhakin kai harin, har zuwa lokacin fassara wadannan labaran.

Tuni jami'an tsaron 'yan sandar kasar ta Sri Lanka suka sanar da cewa sun kame mutane 7 da ake zargin cewa su nada hanu a wadannan jerin hare- hare na ta'addanci.

3805321

 

 

 

 

captcha