IQNA

A Lebanon An Bude Kamfe Na Taimaka Ma Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa a Iran

23:56 - April 19, 2019
Lambar Labari: 3483560
Bangaren kasa da kasa, an bude wani kamfe a kasar Lebanon da nfin taimaka wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Aahad ya bayar da rahoton cewa, a wani taro da aka gudanar a jiya a birnin Beirut na kasar Lebanon, an kaddamar da wani kamfe a kasar Lebanon da nfin taimaka wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a kasar Iran a cikin ‘yan kwanakin nan.

A lokacin da yake gabatar ad jawabinsa a wurin taron, shekh Mahir Hammud, shugaban kungiyar malaman addini masu mara baya ga gwagwarmaya, ya bayyana cewa yana da imanin cewa abin da ya faru jarabawa ta ubangiji, wadda kuma da ikon Allah da taimakonsa al’ummar Iran za su cinye wannan jarabawa.

Dangane da irin matakan da gwamnatin Amurka ta dauka na hana dukkanin kasashen duniya da kungiyoyin bayar da agaji na kasa da kasa zuwa kasar Iran domin taimakawa wadanda ambaliyar ruwan ta rtsa da su, shehin malamin ya bayyana cewa, wannan mataki ya fito da irin bakar siyasar gwamnatin Amurka ta wannan lokaci.

3804934

 

 

 

 

 

captcha