IQNA

MDD: Kimanin Mutane Miliyan 24 Ne Ke Bukatar Taimako A kasar Yemen

22:23 - April 14, 2019
Lambar Labari: 3483547
Bangarena kasa da kasa, majalisar dinkin duniya ta sanar da cewa akalla mutane miliyan 24 ne ke bukatar taimakoa  kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, hukumar bayar da agajin gagwa ta majalisar dinkin duniya ta sanar a cikin wani rahotonta cewa, sakamakon matsalolin da ake fama da su da yaki ya haddasa a Yemen, kimanin mutane miliyan 24 na bukatar taimako.

Bayanin ya ce kimanin kiamnin mutane miliyan 3.3 sun kauracewa yankuannsu, yayin da kuma kashi 51 ne kawai suke iya samun magani da kuma a bangaren kiwon lafiya.

A bangaren yara kuma kashi 25 cikin dari yara kasar ba su samun karatu, kuma ba za su iya zuwa makaranta ba saboda halin da ake cikia  yankunansu.

Tun daga shekara ta 2015 ce Saudiyya ta kaddamr da yaki kan al’ummar kasar Yemen da sunan yaki da ‘yan kungiyar kabilar Huthi, a daidai lokacin da rahotanni majalisar dinkin duniya da na kungiyoyin kasa da kasa suke tabbatar da cewa, dubban fararen hula ne Saudiyya ta kashe  yakin, tare da ragargasa kasar, inda mata da kananan yara suka shiga cikin mawuyacin hali.

3803425

 

captcha