IQNA

An Rusa Gwamnati A Sudan Zanga0Zanga Na Ci Gaba Da Karuwa

23:55 - February 23, 2019
Lambar Labari: 3483399
Bangaren kasa da kasa, Shugaban kasar Sudan ya rusa gwamnatin kasar, tare da kafa dokar ta baci a dukkanin fadin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a jiya ne shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ya gabatar da wani jawabi a jiya wanda aka watsa kai tsaye a dukkanin gidajen radio da talabijin na kasar Sudan, inda ya sanar da rusa majalisar ministoci da kuma gwamnatocin jahohin kasar, tare da kafa dokar ta baci har tsawon shekara guda a dukkanin fadin kasar.

Albashir ya bayyana cewa ministocin harkokin waje, da na tsaro gami da na shari'a za su ci gaba da kasancewa  akan mukamansu, yayin da kuma ya nada wasu manyan jami'an soji 16 da kuma wasu manyan jami'an 'yan sanda biyu a matsayin kantomomi a dukkanin jahohin kasar sha takwas.

A nasu bangaren 'yan adawa sun ci gaba da gudanar da zanga-zanga domin neman Albashir ya sauka daga kan kujerar shugabancin kasar, wadda ya kwashe shekaru 30 a kanta.

Rahotanni sun ce jami'an 'yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa da kuma ruwan zafi wajen tarwatsa masu zanga-zanga a yankin Ummu Durman.

Tun ranar 19 ga watan Disamban 2018 ne aka fara gudanar da wannan jerin gwano a Sudan domin kokawa kan tsadar rayuwa amma lamarin ya koma nuna kyama ga gwamnati.

 

3792430

 

 

 

 

 

captcha