IQNA

Dakarun Somalia Sun Kwace Wasu Kauyuka Biyu Daga Hannun Al-shabab

23:52 - February 23, 2019
Lambar Labari: 3483398
Bangaren kasa da kasa, dakarun kasar Somalia sun samu nasarar kwace wasu kauyuka biyu daga hannun mayakan ‘yan ta’addan Al-shabab.

Kamfanindillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran anatoli ya bayar da rahoton cewa, a yau dakarun kasar Somalia sun sanar da samu nasarar kwace wasu kauyuka biyu wato Hawa Adniyu da Gad Dufar daga hannun mayakan ‘yan ta’addan Al-shabab da suke iko da su tsawon lokaci.

Mayakan kungiyar ta Al-shabab sun janye da kansu a lokacin da suka ga rundunar sojin Somalia ta tunkaro yankin da wadannan kauyuka suke, inda suka fice ba tare da wani artabu ba.

Muhammad Abdullah kakain rundunar sojin Somalia ya bayyana cewa, mayakan Al-shabab sun kasa yin tsayin daka a gaban sojojin Somalia a wadannan kayuka, a kan haka suka yanke shawar arcewa ba tare da wata musayar wuta ba.

3792679

 

 

 

 

captcha