IQNA

Liberman: Firgicin Isra'ila Kan Hamas

21:29 - December 07, 2018
Lambar Labari: 3483193
Bangaren kasa da kasa, Tsohon ministan yakin Isra'ila Ivigdor Liberman ya bayyana cewa, Isra'ila ta nuna tsorata dangane da sha'anin kungiyar Hamas.

kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Almanar ya habarta cewa, tsohon ministan yakin Isra'ila Ivigdor Liberman,a  cikin wani jawabinsa ya bayyana cewa, Isra'ila ta nuna tsorata dangane da Hamas, inda take yin dari-dari wajen fuskantar kungiyar.

Liberman ya cea  cikin watan da ya gabata Hamas ta karbi dala miliyan 15 daga hannun Qatar, a  cikin wanna watan kuma ta harba makamai masu linzami fiye da 500 kan Israila.

Ya ce a cikin watan da ya gabata, jami'an tsaron Isra'ila na Shabak sun kame wasu masu alaka da Hamas a yaniin gabar yamma da Kogin Jordan da suke nufin kai hari kan Isra'ila, a daidai lokacin kuma Hamas ta zartar da hukuncin kisa kan wasu 'yan liken asirin Isra'ila su a cikin zirin Gaza, inda ta harbe su har lahira, ba tare da kuma gwamnatin Isra'ila ta yi tabuka komai ba.

3770217

 

 

captcha