IQNA

Cibiyar Kur’ani A Tunisia Ta Soki Yunkurin Daidaita Maza Da Mata Kan Gado

23:54 - December 06, 2018
Lambar Labari: 3483186
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar kula da harkokin kur’ani a kasar Tunsia ta nuna rashin amincewa da yunkurin daidata maza da mata kan sha’anin gado a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Muhammad saleh Rudaid kakakin cibiyar kula da harkokin kur’ani a kasar Tunsia, ya ce basu mince da yunkurin da gwamnatin kasar ke yi ba, domin ganin an daidata maza da mata kan sha’anin gado.

Ya ce lamarin gado lamari ne wanda Allah ya yi bayaninsa a cikin kur’ani kuma manzon Allah ya aiwatar da shi a  aikace, saboda haka Tunisia a matsayinta na kasar musulmi bai dace da ita ba bin salo na turawa kan sha’anin gado.

Yace a cikin kundin tsarin mulkin kasar Tunisia an amince da addinin muslunci a  matsayin shi ne addinin kasa a hukumance a cikin sassa na 1, 6, 145, 156, saboda haka babu wani dalili na yin gyaran fuska kan batun gado a cikin tsarin mulkin kasar.

A cikin shekarar da ta gabata ce shugaban kasar Tunisia ya gabatar da daftarin kudiri nan a yin daidaito tsakanin mata da maza a sha’anin gado, kuma nan da ‘yan kwanaki masu zuwa ne majalisar dokokin kasar za ta kada kuri’a a kan wannan daftarin kudiri.

3769757

 

 

 

captcha