IQNA

Netanyahu Ya Ce Zai Kai Batun Ramukan Hizbullah A Kwamitin Tsaron MDD

23:13 - December 05, 2018
Lambar Labari: 3483184
Bangaren kasa da kasa, firayi ministan Ira'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa yana shirin kai batun ramukan da ya ce an tona  akan iyakokin Lebanon da Palastine da aka mamaye zuwa ga kwamitin tsaro.

Tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Benjamin Netanyahu firayi ministan Ira'ila ya bayyana cewa yana shirin kai batun ramukan da ya ce an tona  akan iyakokin Lebanon da Palastine da aka mamaye zuwa ga kwamitin tsaron majlaisar dinkin duniya, inda ya ce Hizbullah ce ta tona wadannan ramuka.

Netanyahu ya ce kungiyoyin Hizbullah da Hamas sun ware kasafin kudi mai yawa, domin tona ramuka masu tsawo a karkashin kasa, domin kaddamar da hare-hare a cikin Isra'ila.

Ya kara da cewa, zai batun ga kwaitin tsaro kuma zai nemia  gudanar da zaman gaggawa a kwamitin tsaro kan wannan batu, inda ya ce zai dora alhakin hakan a kan gwamnatin Lebanon wadda ta kasa dakatar da Hizbullah dangane da barazanar da take yi wa Isra'ila.

Tun a ranar Lahadin da ta gabta ce Netanyahu ya aike da sojoji zuwa kusa da iyakokin Lebanon, domin tona abin da ya kira ramukan karkashin kasa na Hizbullah, ayyin da wasu 'yan siyasa a Isra'ila ke cewa Netanyahu yana son ya dauke hankulan Isra'ilawa ne da ma duniya, kan matsalolin da yake fusknata da suka hada da tuhuce-tuhumce na cin hanci da rashawa.

3769758

 

 

 

captcha