Tashar Rusia Yaum ta bayar da rahoton cewa, Kotun kolin da ke da mazauninta a birnin Istanbul ta sanar da cewa, Qahtani da Asiri su ne suke da hannu kai tsaye wajen shirya dukkanin hanyoyin da aka bi wajen kisan Khashoggi.
Kotun ta ce ta bayar da umarni d a kame mata wadannan mutane guda biyu domin gurfanar da su a gabanta kan wannan mummunan laifi da suka aikata.
Ahmad Asiri shi ne shugaban hukumar leken asiri ta kasar Saudiyya, yayin da Qahtani shi ne babban mai bayar da shawara kan harkokin tsaro ga masarautar Saudiyya, kuma na hannun damar Muhammad Bin Salman.
Kotun ta ce mika wadannan mutanen biyu zai taimaka ma Saudiyya ta samu sauki matsin lambar da take fuskanta daga kasashen duniya.